• Rasha Ta Ce Akwai Hanun Amurka A Game Da Hatsaniyar Dake Faruwa A Iran

Shugaban Kwamitin kasa da kasa na Rasha ya ce akwai hanun Amurka dumu-damu kan hatsaniyar dake faruwa a kasar Iran.

A yayin da yake tsokaci a game da hatsaniyar dake faruwa cikin 'yan kwanakin nan a Kasar Iran, Shugaban Kwamitin harakokin kasa da kasa na Rasha Konstantin Kosachev ya ce akwai hanun kasashen waje a game da abin da ke faruwa a kasar Iran.

Jami'in ya ce sanarwar da birnin watsinton ta fitar da kuma firicin Shugaban kasar Amurka Donal Trump a game da masu tayar da hatsaniyar, alama ce dake nuna cewa akwai hanun Amurka kai tsaye kan abinda ke faruwa a kasar ta Iran.

Har ila yau Dan Majalisar na kasar Rasha ya ce Amurka na maraba da duk wani tashin hankali da hatsaniyar da za ta wakana a kasar Iran, kuma a halin da ake ciki, hukumomin Watsinton na cikin shawara da jami'an HK Isra'ila kan hanyoyin da za a bi wajen karin matsin lamba ga jamhuriyar musulinci ta Iran.

Shugaban Kwamitin harakokin kasa da kasa na Rasha ya ce shakka babu, cikin kankanin lokaci za a kawo karshen wannan hatsaniya, kuma duk kasar dake tunani da kuma fatan kawo sauyin gwamnati a Iran, to har abada wannan fata ba zai tabbata ba.

Tun daga ranar Alhamis din da ta gabata ce wasu gungun mutane a garin Mashad suka fito kan titi don nuna rashin jin dadinsu da yadda ake samun tashin farashin kayayyaki a Iran da suke dora alhakin hakan ga tsare-tsaren tattalin arziki na gwamnatin kasar, lamarin da ya watsu zuwa wasu garuruwa na kasar. 

 

Tags

Jan 02, 2018 06:28 UTC
Ra'ayi