• Hukumar Kula Da Zirga-Zirgar Jiragen Sama Ta Duniya Ta Ce Shekara Ta 2017 Tayi Kyau

Shafin yanar gizo ta hukumar kula da tsaro da amincin zirga-zirgar jiragen sama a duniya wato Aviation Safety Network, ta bada rahoton cewa shekarar da ta gabata ta 2017 ita ce shekarar da aka fi samun aminci a zirga-zirgar jiragen sama a duniya a cikin shekaru baya-bayan nan.

Majiyar tashar labarai ta nan JMI ta nakalto hukumar ta Aviation Safety Network tana fadar haka a wani rahoton da ta fitar a bayan shigowar sabuwar shekara kan cewa a shekarar da ta gabata jiragen sama sun tashi daga wurare daban daban a duniya har sau miliyan 36 da dubu 800, amma ma'aunin hatsuran da aka samu a tsawon shekarar, daya ne ga kowane tashi miliyan 7,360,000.

Hukumar ta Aviation Safety Network ta bayyana cewa a duk tsawon shekara ta 2017 an sami hatsarin jirage sau 10 ne kacal. Wannan lissafi dai ya shafi jiragen fasinja ne da kuma na daukar kaya. 

Jan 02, 2018 11:51 UTC
Ra'ayi