Jan 05, 2018 18:57 UTC
  • Amurkawa Suna Dogon Layin Sayen Sabon Littafin Da Aka Rubuta Akan Shugaba Trump

Kamfanin dillancin labaru Associated Press ya nakalto cewa; Mutane sun yi dogayen lakuka a shagunan sayar da littatafai domin su sayi littafin " Fire and Furi" wanda aka rubuta akan Trump

Littafin wanda Micheal Wolfe ya rubuta yana kunshe da bayanai akan shekarar farko ta shugabancin Donald Trump. Kamfanin bugawa da watsa littatafai na Henry Holt ya ce; Saboda ake zumudin littafin an tura lokacin fitar da shi zuwa kwanaki hudu a gaba.

Littafin da aka fare cece-kuce akansa, ya bayyana shugaba Donald Trump a matsayin wanda bai iya mulki ba kuma mai halayya iirn ta yara, kuma bai taba tsammanin cewa zai ci zaben shugabancin kasar ba.

Tuni da shugaba Trump ya yi awashin shigar da kara akan abinda littafin ya kunsa.

Tags

Ra'ayi