• Zarif: Iran Za Ta Ci Gaba Da Riko Da Yajejeniyar Nukiliya Ne Idan Amurka Ta Girmama Ta

Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da ita ne matukar dai Amurka ta ci gaba da girmama yarjejeniyar ba tare da yi mata karan tsaye ba.

Kamfanin dillancin labaran Fars na Iran ya bayyana cewar ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne a ci gaba da ziyarar da yake yi a birnin Mosko, babban birnin kasar Rasha, inda ya ce ci gaba da girmama yarjejeniyar daga bangaren Iran yana da alaka ne da irin yadda Amurka ta ci gaba da girmama yarjejeniyar ba tare da yi mata karan tsaye ba.

Minista Zarif ya ci gaba da cewa: Kowa ya yarda da wajibcin ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliya din, kamar yadda kuma hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta tabbatar da cewa Iran tana ci gaba da girmama yarjejeniyar ta nukiliya, to amma ci gaba da girmama da girmama yarjejeniyar da Iran take yi yana da alaka ne da idan Amurka ta ci gaba da yin hakan.

Ministan harkokin wajen Iran din ya tafi birnin Mosko din ne don ganawa da takwarorinsa na kasashen Rasha, Ingila, Faransa da Jamus bugu da kari kan babbar jami'ar harkokin waje na kasashen Turai, Federica Mogherini don tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliyan musamman bayan barazanar da Amurka take yi na ficewa daga yarjejeniya.

 

Tags

Jan 11, 2018 05:48 UTC
Ra'ayi