• MDD:Cin Mutuncin Da Shugaba Trump Ya Yiwa Afirka Abin Kunya ne

Hukumar kare hakin bil-adama ta MDD ta bayyana cin mutuncin da Shugaba Trump na Amurka ya yi kan al'ummar Afirka a matsayin abin kunya da wariyar launin fata

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Rupert Colville mai magana da yawun babban kwamishinan MDD kan harakokin kare hakin bil-adama a wannan juma'a na cewa fircin da shugaba Trump na Amurka ya yi na cin mutunci ga al'ummar kasashen Afirka da Amurka Latin abin kunya ne kuma wariyar launin fata ne.

Mista  Colville ya tabbatar da cewa wannan lamari bai wai kawai firici na cin mutunci ba, saidai hakan na iya janyo ci gaba da cin mutunci dan Adam da kuma bayar da hanya ga masu ra'ayin wariyar  launin fata da masu kyamar baki su ci gaba da mumunar dabi'arsu.

A ranar Alhamis ne, shugaba Trump ya ce bai ga dalilin da Amirka za ta karbi 'yan gudun hijira daga kasashen Haiti da Afirka ba wadanda ya kira da taron tsintsiya ba shara, a maimakon haka gara kasar ta karbi 'yan gudun hijira daga kasar Norway wadanda ya bayyana da cewar mafiya yawan su farar fata ne.

Har ila yau wannan furuci da Trump ya yi kan kasashen Haiti da Afirka ya fusata 'yan siyasa daga Jam'iyyun Democrats da kuma Republican a fadin kasar inda su ka yi zarginsa da rura wutar wariyar launin fata.

Tags

Jan 12, 2018 19:10 UTC
Ra'ayi