Feb 09, 2018 06:37 UTC
  • Kwamitin Tsaron MDD Ya Tattauna Matsalolin Da Suke Ci Gaba Da Addabar Kasar Siriya

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kawo karshen zamansa kan matsalolin da suke ci gaba da addabar kasar Siriya ba tare da daukan wani mataki ba a jiya Alhamis.

Kasashen Sweden, Faransa da Kuwait da suke cikin mambobin kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a wannan karo ne suka gabatar da daftarin kuduri kan bukatar gudanar da zaman taron kwamitin tsaron dangane da matsalolin da suke ci gaba da addabar kasar Siriya bayan da kungiyoyin bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya suka gabatar da rahotonninsu kan halin tsaka mai wuya da al'ummar Siriya suke ciki.

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya tattaunawa batun tarin matsalolin na Siriya ba tare da daukan wani mataki domin magance su ba. Gwamnatin Siriya dai ta sha aikewa da sakonni kan yadda jiragen saman yakin kasar Amurka karkashin rundunar kawancenta kan yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar ta Siriya suke yin luguden wuta kan al'ummar Siriya musamman kan sansanonin sojin gwamnatin kasar da nufin bai wa gungun 'yan ta'addan kasa da kasa damar da ci gaba da wanzuwa a cikin kasar. 

Tags

Ra'ayi