• Jakadan Iran A Nijeriya: Gabatar da Tsarin Demokradiyya Na Addini Na Daga Cikin Nasarorin Juyi Musulunci na Iran

Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Nijeriya, Mortadha Rahemi, ya bayyana cewar gabatar da tsarin demokradiyya na addini daya ne daga cikin nasarori masu muhimmancin gaske da juyin juya halin Musulunci na Iran ya samu.

Kamfanin dillancin labaran Fars na Iran ya bayyana cewar, jakadan Iran a Nijeriya din, Mortadha Rahemi, ya bayyana hakan ne a wajen bikin tunawa da shekaru 39 da nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran da aka gudanar a birnin Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriyan inda ya ce tsawo wadannan shekaru 39 an gudanar da zabubbuka 40 a kasar Iran wanda hakan ke nuni da irin yadda tsarin demokradiyya na addini ya samu kafuwa a kasar.

Yayin da yake magana kan alakar Nijeriya da Iran kuwa, Mr. Rahemi ya ce alakar tana kara karfi yana mai ishara da irin karuwar alaka da kuma ziyarar da jami'an kasashen biyu suka kai wa juna a shekarar da ta gabata ta 2017, inda ya ce a nan gaba kadan ma za a gudanar da taron kwamitin aiki tare a fagen kasuwanci da tattalin arziki na shida tsakanin kasashen biyu.

A ranar 11 ga watan Fabrairun 1979 ne dai juyin juya halin Musulunci na Iran din karkashin jagorancin marigayi Imam Khumaini (r.a) yayi nasara da kuma kawo karshen gwamnatin kama karya ta sarki Shah na kasar. A duk shekara idan wannan rana ta zagayo a kan gudanar da bukukuwa a ciki da wajen Iran don murnar wannan nasara. 

Tags

Feb 12, 2018 17:58 UTC
Ra'ayi