Feb 13, 2018 16:41 UTC
  • Sabon Zargin Tawagar MDD Da Lalata A (DRC)

Tawagar MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar demokuradiyar Congo ta karbi rahotannin wasu zarge-zargen aikata ba daidai ba, ciki har da wasu laifukan yin lalata guda uku da ake zargin ma'aikatan nata da aikatawa.

Kakakin MDD Stephane Dujjaric shi ne ya bayyana hakan, yana mai cewa wadannan zarge-zarge sun shafi sojojin kasar Afirka ta kudu dake aikin wanzar da zaman lafiya.

An dai aikat alaifukan ne a garuruwan Sake, da Beni, da Goma dake arewacin lardin Kivu.

Mista Dujaric ya ce, yanzu haka asusun kula da yawan jama'a na MDD yana kokarin tabbatar da cewa, an taimakawa wadanda aka ci zarafin nasu ba tare da bata lokaci ba.

Kakakin ya ce, zargi na hudu ya shafi wani yaro dan shekara 17 ne da sojojin kiyaye zaman lafiya suka ci zarafinsa a gabashin lardin Kasai. 

Tags

Ra'ayi