Feb 13, 2018 17:13 UTC
  • Amurka : Farmakin Turkiyya A Siriya, Ya Raunana Yaki Da IS_Tillerson

Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, ya bayyana cewa farmakin da Turkiyya ke kaiwa kan mayakan Kurdawa a arewacin Siriya, ya raunana yakin da ake da kungiyar 'yan ta'adda ta IS.

Mista Tillerson, ya ce farmakin na Turkiyya ya cilastawa mayakan Kurdawa abokan tafiyar Amurka komawa yankin Afrin.

Da yake ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Kowait bayan a yayin wani taron kawacen kasa da kasa na yaki da ta'addanci, Tillerson ya ce zai kai ziyarci kasar ta Turkiyya a wannan mako domin tattauna da mahukuntan kasar ta yadda zasu ci gaba da aiki tare.

A ranar 20 ga watan Janairu da ya gabata ne Turkiyya ta kaddamar da gagarimin farmaki kan mayakan Kurdawa na (YPG), da ta ke dangantawa da 'yan ta'adda.

Dama kafin hakan Mista Tillerson ya bukaci bangarorin biyu da su kai zuciya nesa, su maida hankali kan yaki da ta'addancin kungiyar IS.

Tags

Ra'ayi