Feb 14, 2018 06:17 UTC
  • Faransa: Idan Amfani Da Makaman Guba A Kan Fararen Hula Ya Tabba A Kasar Siria Faransa Zata Kai Mata Hari

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa a duk lokacin da ya tabbata a gareshi kan cewa gwamnatin kasar Siria ta yi amfani da makaman guba kan fararen hula a kasar, gwamnatinsa zata kai hari kan wuraren da aka harhada makaman a kasar Sirya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Macron yana fadar haka a jiya, inda ya kara da cewa ya zuwa yanzu babu wata shaida da ta tabbatar da cewa gwamnatin kasar Siria ta yi amfani da irin wadannan makamai.

Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka da ta Britania sun tada maganar cewa sojojin kasar Syria sun yi amfani da makaman guba kan fafaren hula a yakin da take fafatawa da yan ta'adda a kasar. Amma gwamnatin kasar Siria ta musanta zargin. 

Har'ila yau shugaban Macron ya bayyana cewa ya tattauna da shugaban Putin na kasar Rasha kan wannan batun ta wayar tarho a ranar juma'a nan da ta gabata, ya kuma bukace shi da ya isarwa gwamnatin kasar Siria sakon cewa suna sanya ido a kan ayyukan sojojinsa.

Wannan ba shi ne karon farko wanda wadannan kasashe suke zargin gwamnatin kasar Siria da amfani da irin wadannan makamai ba. Banda haka gwamnatin ta kasar Siria ta mika dukkan makamanta na guba ga tawagar MDD a shekara ta 2014.

 

Tags

Ra'ayi