• Koriya Ta Kudu Ta Bukaci Amurka Ta Sassauta Bukatunta Ga Koriya Ta Arewa

Shugaban Koriya ta Kudu, Moon Jae-in, ya bukaci Amurka da ta sassauta bukatunta don samun tattaunawa da mahukuntan Pyongyang.

Mista Moon, ya ce yana ganin kamata ya yi Amurka ta dan sassauta akan manufofinta, ko walla Allah hakan zai bude kofar tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, amma kuma yana da kyau ita ma Koriya ta Arewa ta gwada da gaske ta ke akan kwance shirinta na nukiliya.

Wanan dai ya biyo bayan da aka samu 'yar jituwa tsakinin kasashen Koriya ta Arewa data Kudu a baya bayan nan musamman a wasanin gasar Olympics ta Hunturu, idan Koriya ta arewar ta aike da tawagogi da ta wasu manyan Jmai'an kasar a wasannin na bana.

Shugaba Moon, ya ce yana da matukar mahimmanci AMurka da Koriya ta Arewa su zaina tabeburun tattauna a lokacin da ya tsawaka, tare da kiran ga mahukuntan Pekin akan su dukufa kan hakan.

Tags

Feb 26, 2018 11:18 UTC
Ra'ayi