• Amurka : Trump, Ya Yi Maraba Da Tayin Koriya Ta Arewa Na Tattaunawa

Shugaba Donald Trump na Amurka, ya yi maraba da matakin gwamnatin Koriya ta Arewa kan yiwuwar bude kofar tattaunawa da kasarsa, amma tare da kiran a yi taka tsantsan har a samu tabbaci kan matakin.

Koriya ta kudu ce dai ta sanar da wannan anniyar ta makobciyyar ta Koriya ta Arewa bayan ganawar mahukuntan kasashen biyu a birnin Pyongyang. 

A cewar mahukuntan na Seoul, Koriya ta Arewa a shirye take ta tattauna da Amurka kan batutuwa masu tsarkakiya da ake dade ana takadama akansu ciki har da shirin Koriya Ta Arewar na nukiliya.

Shugaba Trump ya ce abu ne mai kyau ga duniya, ga Koriya ta Arewar ga yankin, amma zamu zura ido mu gani abunda zai faru, tare da cewa shi ya kamata a jinjinawa kan wannan ci gaba.

Koriya ta Arewa dai ta jima tana fama da jerin takunkumi na kwamitin tsaron MDD, kan gwaje gwajen makammanta na nukiliya da masu linzami dake cin dogon zongo.

Tags

Mar 07, 2018 05:48 UTC
Ra'ayi