• Yariman Saudiyya Ya Fara wata Ziyara A Kasar Birtaniya

Yariman Saudiyya mai jiran gado Muhamman Bin Salman ya fara wata ziyara a kasar Birtaniya a yau Laraba.

Bin Salman ya isa kasar ta Birtaniya ne bayan ya kammala zirar da kai a kasar Masar. A yayin ziyarar tasa a Birtaniya zai gana da manyan jami'an gwamnatin kasar, da suka hada firayi minista Theresa May, da kuma sarauniya Elizabeth.

Birtaniya na daga manyan kasashen Saudiyya da suke ba ta kariya a siyasance da kuma ta fuskar tsaro, inda a ziyarar tasa Muhammad Bin Salman zai sanya hannu kan wani shirin hadin gwiwa na saka hannun jari tare da Birtaniya, wanda zai kai dala biliyan 100, kuma za a aiwatar da shia  cikin shekaru 10.

Da dama daga cikin 'yan siyasa da kungiyoyin farar hula da masu kare hakkin bil adama da ma wasu kungiyoyin musulmi a kasar ta Birtaniya, suna ta yin tir da Allah wadai da wannan ziyara, inda ake sa ran za a gudnar da gangami da jerin gwano a birnin London da ma wasu biranan kasar domin yin tir da Allah wadai da wanann ziyara ta Muhammad Bin Salman, wanda suke bayyana da shi da dan kama karya, da kuma kisan mata da kananan yara a Yemen.

Mar 07, 2018 17:05 UTC
Ra'ayi