• Corbyn: Sayarwa Saudiyya Da Makamai Domin Yaki A Kan Yemen Abin Kunya Ne Ga Birtaniya

Shugaban jam'iyyar Labour a kasar Birtaniya Jeremy Corbyn, ya bayyana cewa; sayarwa Saudiyya da manyan makamai da Birtaniya take domin kaddamar da yaki a kan al'ummar kasar Yemen, babban abin kunya ne ga gwamnatin Birtaniya.

Tashar talabijin ta Sky News ta bayar da rahoton cewa, a lokacin zaman majalisar Birtaniya a yau Jeremy Corbyn ya bayyana cewa, bai kamata Birtaniya da ke ikirarin bin tafarkin dimukradiyya ta zama mai mara baya ga ayyukan kisan bil adama ba, domin kuwa dukkanin makaman da ta sayar wa Saudiyya a cikin 'yan lokutan nan, an yi amfani da su wajen kisan mata da kananan yara a Yemen.

Ya ce dole ne firayi ministan kasar ta Birtaniya ta yi amfani da ziyarar da yariman Saudiyya ya fara gudanarwa a kasar yau, wajen dakatar da Saudiyya daga kisan dubban fararen hula a Yemen.

A cikin shekaru da suka gabata daga lokacin da Saudiyya ta fara kaddamar da hare-hare kan al'ummar kasar Yemen da sunan yaki da 'yan kungiyar Alhuthi, ya zuwa yanzu Birtaniya ta sayarwa Saudiyya makamai da aka yi amfani da su a wannan yaki da suka kai na dala biliyan 6.4, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula fiye da 13,600 bisa kididdigar kungiyoyin kasa da kasa.

Tags

Mar 07, 2018 17:16 UTC
Ra'ayi