• Ziyarar Sakataren Harkokin Kasashen Wajen Amurka Zuwa Nahiyar Afirka

A jiya Laraba ne sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, ya fara ziyararsa a nahiyar Afirka inda aka tsara zai ziyarci kasashen da suka hada da Ethiopia, Djibouti, Kenya, Chad da kuma Nijeriya a daidai lokacin da gwamnatin Donald Trump ta Amurka take ci gaba da shan suka sakamakon rashin wata fitacciyar siyasa da take da shi dangane da ci gaban Afirkan.

Kafin fara ziyarar dai, sakataren harkokin wajen na Amurka ya bayyana cewar: Babu wani lokaci tsawon tarihi da tsaro da ci gaban tattalin arzikin Amurka  suke da alaka da kasashen Afirka kamar wannan zamanin. To sai dai a daidai lokacin da babban jami'in diplomasiyyar Amurkan yake magana kan muhimmancin da Afirkan take da shi ga Amurka, a daidai lokacin da irin mu'amala da maganganun da shugaban Amurkan Donald Trump yake yi da nahiyar Afirka ba ta nuni da irin wannan muhimmancin da sakataren harkokin wajen Amurkan yake kokarin nunawa. Idan ba a mance ba 'yan makonnin da suka gabata ne shugaba Trump din ya bayyana kasashen Afirkan a matsayin wasu wulakantattun kasashen, lamarin da ya fuskanci fushi da kuma tofin Allah tsine daga dukkanin kasashen Afirka, da kuma kiran jakadu da jami'an diplomasiyyar da suke Afirka don nuna musu rashin amincewa da wadannan kalamai na shugaban Amurkan.

Wani lamarin kuma ya kara hada gwamnatin Trump din da kasashen Afirka shi ne rashin goyon bayan da shugabannin Afirkan suka nuna wa shirin Amurka na mayar da ofishin jakadancinta da ke HKI zuwa birnin Qudus bayan da ta sanar da birnin Qudus din a matsayin babban birnin HKI.

A saboda haka ne da dama suke ganin babbar manufar wannan ziyara ta Rex Tillerson ita ce kokari wajen dinke wannan baraka da ta kunno kai tsakanin Amurkan da kasashen Afirkan, musamman a daidai wannan lokaci da Amurkan take fuskantar matsaloli na siyasa da tattalin arziki sakamakon irin siyasar gwamnatin Trump din wacce take ci gaba da sanya alakar Amurka da sauran kasashen duniya hatta kawayenta na kasashen Turai cikin mawuyacin hali da kuma ci gaba da yin tsami.

Haka nan a bangaren tsaro ma dai sakamakon irin yaduwar ayyukan ta'addanci da ake fuskanta a nahiyar Afirka, musamman irin ci gaba da kwararar da 'yan ta'adda musamman 'yan kungiyar ISIS da suke ci gaba da shan kashi a Siriya da Iraki suke yi zuwa nahiyar Afirkan, dukkanin wadannan suna daga cikin batutuwan tsaro da suke damun Amurkan, watakila ba wai dole manufar ta zamanto ita ce kawo karshensu gaba daya ba, face dai babban abin da Amurkan take son samu shi ne yin tasiri a kansu da irin juya su yadda take so bisa la'akari da cewa da dama daga cikin irin wadannan kungiyoyi kirar Amurkan ce da kanta don cimma manufofin da take so.

Ko shakka babu irin ci tasiri da kuma kutsawar da kasar China ta samu a nahiyar Afirkan da ya sanya ta ta zamanto kasar da take kan gaba wajen alaka ta kasuwanci da Afirkan ta hanyar zuba jari da kuma sayar da kayayyakinta ga kasashen Afirkan, wannan lamari na daga cikin abubuwan da suke kara ci wa Amurkan tuwo a kwarya sannan kuma tana ganin hakan a matsayin barazana ga alakarta ta tattalin arziki da nahiyar Afirkan. Don haka daya daga cikin manufar wannan ziyarar ita ce kokari wajen rage irin wannan tasiri da China ta samu a nahiyar Afirkan.

To sai dai abin tambaya a nan shi ne shin gwamnatin Amurkan, musamman a wannan lokaci na shugabancin Trump da ba ya ganin kowa da gashi, za ta iya cimma wannan manufa na ta kuwa? Abin dai da kamar wuya.

Tags

Mar 08, 2018 05:24 UTC
Ra'ayi