• Rasha Ta Yi Suka Kan Tsoma Bakin Kasar Amurka A Harkokin Siyasar Kasashen Duniya

Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Tsoma bakin da kasar Amurka take yi a harkokin siyasar kasashen duniya, wani nau'in mulkin kama karya ne kan kasashen.

A ziyarar aikin da ya kai zuwa Zimbabwe; Ministan harkokin wajen kasar Rasha Seigei Lovrof ya gana da shugaban kasar Emmerson Mnangagwa a yau Alhamis, inda suka tattauna kan batun gudanar da taimakekkeniya kan harkar soji tare da bunkasa alakar tattalin arziki a tsakanin kasashensu.      

Har ila yau a taron manema labarai da ya gudanar da takwaransa na kasar ta Zimbabwe a birnin Harare a yau Alhamis: Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lovrof ya bayyana cewa: Al'adar Amurka ce tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen duniya musamman a harkokin siyasarsu tare da kokarin juya akalar kasashen domin samun damar cimma manufofinta musamman a harkar tattalin arziki.

 

Tags

Mar 08, 2018 19:04 UTC
Ra'ayi