• Kungiyar Al-Qa'ida Ta Yi Gargadin Kaddamar Da Hare-Hare Kan Sojojin Faransa

Cibiyar rundunar sojin Amurka da ke sanya ido kan shafukan kungiyoyin 'yan ta'adda ta bada labarin cewa: Kungiyar ta'addanci ta Al-Qa'ida a yankin arewacin Afrika ta yi gargadin cewa zata fara kaddamar da hare-hare kan sojojin Faransa da suke yankin.

Cibiyar rundunar sojin Amurka da ke sanya ido kan shafukan sadarwa mallakin kungiyoyin 'yan ta'adda a duniya ta bayyana cewa: Shugaban kungiyar Al-Qa'ida Ayman Azzawahiri ya fitar da sako ta hanyar fyaifyan bidiyo da ke bayyana cewa: Mayakan kungiyarsa zasu dauki matakin zafafa kai hare-hare kan sojojin Faransa da suke yankin arewacin Afrika.

Cibiyar kasar ta Amurka ta kara da cewa: Matukar wannan barazana ta shugaban kungiyar Al-Qa'ida Ayman Azzawahiri ta tabbata, to babu shakka sojojin Faransa da suke yankin zasu shiga cikin mummunar kangi.

 

Mar 08, 2018 19:04 UTC
Ra'ayi