• Rasha Ta Ce Za Ta Mayar Da Martani Idan Amurka Ta Kai Hari Siriya

Wani babban jami'in sojin kasar Rasha ya bayyana cewar sojojin Rashan za su mayar da martani ga duk wani harin da sojojin Amurka za su kai kasar Siriya matukar dai harin ya zamanto barazana ga rayuwar sojojin Rashan da suke Siriya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Rashan RIA ya jiyo Janar Valery Gerasimov yana fadin cewa akwai masu ba da shawara 'yan kasar Rasha a kasar Siriyan bugu da kari kan wakilan cibiyar sasantawa ta kasar Rasha da kuma wasu sojojin kasar a birnin Damaskus, kamar yadda akwai wasu kuma a cibiyoyin tsaron kasar Siriya, don haka ya ce matukar Amurka ta kai hari irin wadannan wajaje to kuwa Rasha za ta mayar da martani ga cibiyoyin da aka harbo irin wadannan makamai zuwa Siriyan.

Wannan jan kunnen dai ya zo kwana guda bayan da jakadiyar Amurka a MDD Nikki Haley ta ce Amurka a shirye take ta yi gaba gadi wajen kai wa Siriya hari kamar yadda ta yi a baya dangane da batun amfani da makamai masu guba; lamarin da tun a lokacin Rashan ta ki amincewa da shi.

A jiya Litinin ma dai, jakadan Siriyan na MDD Bashar al-Ja’afari yayi tofin Allah ga wannan sabon barazanar Amurka, yana mai cewa wadannan maganganu na Haley wani kokari ne na kwadaitar da 'yan ta'adda yin amfani da makamai masu guban daga baya kuma Amurkan  ta zargi Siriya da yin hakan.

Mar 13, 2018 11:17 UTC
Ra'ayi