• Jami'an Tsaron Kasar Mexico Sun Kame Mutumin Da Ake Zargi Da Kashe Dalibai 43

Ma'aikatar shari'ar kasar Mexico ta sanar da kame shahararren mai fataucin muggan kwayoyi a kasar da ake zargi da hannu a kashe daliban makaranta 43 a shekara ta 2014.

Ofishin babban lauyan gwamnati mai shigar da kara a kasar Mexico ya sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar kame Erick N shahararren mai fataucin muggan kwayoyi a kasar, kuma mutumin da ake zargi da hannu a kashe daliban makarantar kwalejin horas da malaman makarantun boko ta Ayotzinapa a shekara ta 2014 bayan tsawon shekaru uku da rabi ana farautarsa.

Ofishin babban lauyan gwamnatin kasar ta Mexico ya kara da cewa: Akwai yiyuwar Erick N mamba ne a gungun 'yan daba masu aiwatar da muggan laifuka da suka hada da fataucin muggan kwayoyi a jihar Guerrero da ke shiyar kudu maso yammacin kasar Mexico.

Bincike yana nuni da cewa: Tun a shekara ta 2014 ce daya daga cikin gurbatattun 'yan sandan Mexico ya sace daliban makarantar horas da malamai ta Ayotzinapa guda 43 tare da mika su ga Erick N, inda ya aiwatar da kisan gilla kansu tare da kona gawawwakinsu, sannan ya zuba tokar gawawwakin a cikin teku.  

Tags

Mar 14, 2018 06:31 UTC
Ra'ayi