• An Sake Zaben Angela Merkel A Matsayin Waziriyar Jamus A Karo Na Hudu

'Yan majalisar dokokin kasar Jamus sun zabi Angela Merkel a matsayin waziriya kuma shugabar gwamnatin kasar a karo na hudu mai yiyuwa kuma na karshe na mulkinta a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar a yau Laraba ce a zaman da 'yan majalisar suka gudanar suka kada kuri'ar amincewa da Angela Merkel din da ta ci gaba da shugabancin gwamnatin kasar a karo na hudu bayan tsaiko da aka samu na dan wani lokaci sakamakon washin cimma yarjejeniyar tsakanin jam'iyyun da suke da kujeru a majalisar kasar.

Sakamakon kuri'ar da aka kada din dai na nuni da cewa Angela Merkel din ta sami kuri'u 364 da suka amince da ita, wasu 315 kuma suka nuna rashin amincewa alhali wasu guda tara kuma sun ki kada kuri'ar tasu.

Jim kada bayan kada kuri'ar dai waziriya Merkel, 'yar shekaru 63 a duniya ta sanar da amincewarta da ci gaba da shugabancin gwamnatin Jamus din duk kuwa da matsalolin da za ta iya fuskanta ganin cewa gwamnatin nata ba ta da rinjaye sosai a majalisar.

 

Tags

Mar 14, 2018 11:06 UTC
Ra'ayi