• Iran Ta Yi Kira Da A Hana Kara Cutar Da Musulmin Rohingya

Wasu 'yan Majalisar shawarar musulunci ta Iran biyu da suke ziyartar kasar Thailand sun yi kira da a hana afkuwar wani bala'in akan al'ummar musulmin Rahingya na kasar Myanmar

Gulam Ridha Katib da Ba'uj Lahuti, sun bayyana hakan ne a lokacin da suka gana da shugaban Majalisar dokokin kasar Thailand Vijita Jolajayi.

Har ila yau 'yan majalisar sun bayyana wajabcin samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai da al'ummu mabanbanta.

Wannan ba shi ne karon farko da jamhuriyar musulunci ta Iran take yin kira domin warware matsalar musulmin Rohingya ba da hana a ci gaba da cutar da su.

Tags

Mar 16, 2018 06:19 UTC
Ra'ayi