Mar 19, 2018 06:38 UTC
  • Sharhi: Putin Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Rasha Da Tazara Mai Yawa

A jiya ne aka gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Rasha, wanda sakamakon zaben ya yi nuni da cewa shugaba Vladimir Putin mai ci ne ya lashe shi da tazara mai nisan gaske tsakaninsa da sauran abokan hamayyarsa 7, bayan da aka sanar da sakamakon mafi yawan mazabu, wanda a jimilla Putin ya samu kashi 76.6 cikin dari.

Vladimir Putin mutumin da Rashawa ke yi masa kirari da (Gawurtacce)  zai sake yin wani wa'adin mulki karo na hudu kuma na shekaru shida  a nan gaba.

A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a jiya bayan kada kuri'arsa, shugaba Putin ya bayyana cewa, zai amince da duk wani sakamako na kuri'ar da al'ummar Rasha suka kada, idan kuma har ya samu nasarar lashe zaben, to zai mayar da hankali kan muhimman batutuwa da suke a gabansa, wato ci gaba da inganta rayuwar al'ummar Rasha, da kuma kara karfafa tsaro domin kare kasar daga duk wata barazana daga makiyanta.

Fiye da mutane miliyan 109 ne suka cancanci kada kuri'a a kasar Rasha, kuma hukumar zaben kasar ta ce kimanin kashi 65% na wadanda suka cancanci kada kuri'ar ne suka halarci zaben.

Zaben na Rasha ya zo ne a daidai lokacin da kasashen yammacin turai suke ta kara matsa lamba kan kasar, sakamakon irin matakan da Putin yake dauka  a kan lamurra da dama a fagen siyasar duniya, wadanda suka yi hannun riga da manufofin siyasar kasashen yammacin turai, wanda kuma kasashen yammacin turai suna kallon salon siyasar Vladimir Putin a matsayin babban karfen kafa da ke kawo musu babban cikas wajen cimma manufofinsu a kan al'ummomin duniya.

Abubuwan da suke wakana a cikin 'yan shekarun nan a kasashen larabawa, inda kasashen yammacin turai suke yin amfani da 'yan ta'adda wajen rusa kasashe da gwamnatocinsu da ba su yi musu biyayya, na daya daga cikin abubuwan da suka kara jawo takun saka a tsakanin Rasha da kuma kasashen yammacin turai, musamman kan batun Syria, inda kasashen turai gami da Isra'ila suka dage sai sun kifar da gwamnatin Syria wadda ba su dasawa da ita, kamar yadda suka yi a Libya, ta hanyar yin amfani da 'yan ta'adda masu dauke da akidar takfiriyya, da kuma yin amfani da wasu kasashen larabawa masu yin biyayya ga turawa ido rufe wajen daukar nauyin 'yan ta'addan, tare da bayar makudan kudaden da ake bukata domin aiwatar da wannan manufa.

Dukkanin kasashen turai sun kwana da sanin cewa yin fito na fito da Rasha ta hanyar yin amfani da karfin soji ba abu ne mai yiwuwa ba, a kan haka suka fifita yin amfani da hanyoyi na matsin lamba da saka takunkumi a kan kamfanoni da cibiyoyi na Rasha da nufin gurgunta ta, wanda kuma hakan babu abin da yake karawa Rasha sai jajircewa da kuma yin nisa mai tazara a tsakaninta da turawa.

A cikin 'yan kwanakin nan a lokacin da ake shirin gudanar da zaben Rasha, kasashen Amurka da Birtaniya, sun hura wutar tsangwama a kan Rasha da nufin yin tasiri a zaben shugaban kasar, ta yadda hakan zai rage farin jinin shugaba Putin, to amma kuma hakan bai kara masa komai ba sai kwarjini da kara samun karbuwa a tsakanin al'ummar Rasha, wadanda suke kallonsa  a matsayin mutumin da ya dawo wa kasar da karfinta da matsayinta da martabarta a idon duniya, tun bayan da kasashen yammacin turai suka rusa tarayyar Soviet.

Tags

Ra'ayi