Mar 21, 2018 06:42 UTC
  • Amurka:Sanatoci Sun Amince Da Ci Gaba Da  Goyon Bayan  Saudiya A Yaki Da Yemen

A jiya talata majalisar datijan kasar Amurka ta yi watsi da wani kuduri da aka gabatar mata na dakatar da goyon bayan saudiya a yaki da kasar Yemen

Wannan kuduri na zuwa ne a yayin da ministan tsaron kasar Saudiya kuma yarima mai jiran gado Muhamad bn salman ke ziyara a kasar ta Amukra, inda a jiya talata ya gana da shugaba Trump tare da sanya hannu kan yarjejjeniyar sayan makamai na makudan kudade.

Kafin 'yan majalisar dattijan Amurka suka wannan kuri'a ta kin amincewa da dakatar da gwamnatin Amurkan  goyon bayan da take bawa saudiya kan ci gaba da ta'addanci a yemen, gwamnatin Amurka ta nuna adawa da wannan kuduri, inda ministan tsaron kasar James Mattis ya ce zasu kalubalanci wannan kudiri a majalisar dattijan kasar.

Tun a watan Maris na shekarar 2015 ne kasar Saudiya bisa cikekken goyon bayan saudiya da haramtacciyar kasar Saudiya ta kadamar da yakin wuce gona da iri kan al'ummar Yemen tare da killace kasar ta kasa, ruwa da kuma sararin samaniya bisa da'awar dawo da gwamnatin tsohon shugaban kasar da ya yi murabus Abdu Rabahu Mansoor Hadi.

Tags

Ra'ayi