Mar 22, 2018 05:20 UTC
  • An Gabatar Wa Sarkozy Cajin Zargin Karbar Kudaden Yakin Neman Zabe Daga Gaddafi

Ma'aikatar shari'ar kasar Faransa ta sanar da tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy a hukumance fara gudanar da bincikensa dangane da zargin da ake masa na karbar miliyoyin Euro daga wajen tsohon shugaban kasar Libiya Mu'ammar Gaddafi don yakin neman zabensa a shekara ta 2007.

Kamfanin dillancin labaran The Associated Press ya bayyana cewar wata majiyar shari'ar kasar Faransa ta shaida masa cewar a jiya Laraba ce alkalan da suke gudanar da bincike suka gabatar wa Mr. Sarkozy da takardar cajin da ake masa na amfani da kudin haramun wajen gudanar da yakin neman zabensa, ta hanyar karbar kudade daga kasar Libiya.

Rahotanni sun ce an gabatar wa Sarkozy da wadannan takardun zargin ne bayan kwanaki biyu na tambayoyin da 'yan sanda masu fada da rashawa da cin hanci na kasar Faransa suka yi masa dangane da zargin da ake masa cewa ya karbi kudaden da suka kai Euro miliyan 50 (kimanin dollar miliyan 62) daga wajen Gaddafi don amfani da su wajen yakin neman zabensa lamarin da ya saba wa dokokin kasar Faransan.

Mr. Sarkozy dan shekaru 63 a duniya dai ya musanta wannan zargin. Bayan binciken dai an sako shi ya dawo gida sai dai kuma karkashin sanya idon ma'aikatar shari'a din wacce za ta ci gaba da gudanar da binciken wanda daga karshe akwai a gurfanar da shi a gaban kotu.

Sarkozy din dai yana daga cikin shugabannin kasashen Turai da suka jagoranci kifar da gwamnatin Gaddafin a shekara ta 2011.

 

Tags

Ra'ayi