Apr 02, 2018 06:27 UTC
  • Trump Ya Yi Barazanar Korar Bakin Haure Kimanin Dubu Biyu

Shugaban kasar Amurka ya dage tsugunar da 'yan gudun hijra kimanin miliyan daya da dubu dari takwas tare da bukatar daukan tsauraren matakai na kare iyakokin kasar.

Bayan kwashe watani ana tattauanawa da 'yan majalisar dattijan kasar kan batun kudaden da za a kashe na gina katanga tsakanin Amurka da Maxico ba tare da cimma matsaya ba,shugaba Trump ya ce ba zai ci gaba da aiki da dokar Daka ba, Daka doka ce dagwamnatin da ta shude ta Barak Obama  ta samar da ta bayar da damar daukan nauyin wani gungun bakin haure da suka shiga kasar Amurkan tun suna yara.

A makon da ya gabata ne, shugaba Trump ya sanya hanu kan kasafin kudin 2018 ba tare da cimma matsaya kan dokar Daka ba.

Kasafin kudin wannan shekara na kasar Amurka ya samu amincewa ne a majalisar dattijan kasar bayan da aka cire kaso mafi yawa na kudaden da kasar ke kashewa na gina katangar iyaka da kasar Maxico, lamarin da ya fusata shugaba trump ya dauki wannan mataki.

Tags

Ra'ayi