• Basshar Asad: Za a Ci Gaba Da Fada Da Ta'addanci Har Sai An Tsarkake Siriya Daga 'Yan Ta'adda

Shugaban kasar Siriya Basshar al-Asad ya bayyana cewar fada da ta'addanci zai ci gaba da a kasar har sai lokacin da aka tsarkake dukkanin kasar Siriya daga 'yan ta'adda.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran IRNA ya bayyana cewar shugaba Asad din ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan lamurran siyasa Husain Jabiri Ansari wanda ya kai masa ziyara a fadarsa da ke birnin Damaskus, inda yayin da yake ishara da harin wuce gona da irin da Amurka da Faransa da Ingila suka kai kasar a kwanakin baya, ya bayyana cewar: Harin da suka kai din kai tsaye kan kasar Siriya ba zai dakatar da fada da ake yi da ta'addanci ba.

Shugaba Asad ya ci gaba da cewa: Wadannan kasashen da ma wasu kasashen yankin Gabas ta tsakiya tun ranar farko suke goyon bayan 'yan ta'adda kuma har yanzu ma suna ci gaba da yi.

Shi ma a nasa bangaren Mr. Ansari ya bayyana cewa dalilin harin da Amurka da kawayenta suka kai Siriyan shi ne saboda irin nasarorin da sojojin Siriyan suke samu a kan 'yan ta'addan.

Tags

Apr 23, 2018 17:34 UTC
Ra'ayi