Apr 24, 2018 11:04 UTC
  • Ana Taron Nema Wa 'Yan Gudun Hijira Siriya Tallafi

Kasashen duniya na wani taro a birnin Brussels, mai manufar tattara tallafi wa 'yan gudun hijira Siriya.

Taron na da gurin hada tallafi don taimaka wa 'yan Siriya miliyan biyar dake gudun hijira da kuma wasu sama da miliyan shida dake cikin gida.

Wannan shi ne taro irinsa na bakwai dake hada masu bada tallafi da kungiyoyin agaji na kasa da kasa da na MDD, ke taron don nema wa 'yan gudun hijira Siriya tallafi.

A bara dai taron ya tattara kudaden tallafi da ya kai dalar Amurka bilyan shida ga 'yan kasar ta Siriya dake fama da yakin basasa.  

Tags

Ra'ayi