Mayu 21, 2018 15:51 UTC
  • Amurka Ta Yi Barazanar Kakaba Wa Iran Takunkumai Mafi Tsanani A Tarihi

Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya sanar da sabbin dabarun Amurka wanda ya ce su ne mafi tsanani a tsawan tarihi, don matsin lamba wa Iran, idan bata amince sharuddanta ba.

Wannan dai na zuwa ne makwanni kadan bayan da shugaba Donald Trump ya sanar da janye Amurkar daga yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma wa da Iran a 2015. 

Da yake sanar da hakan a yau Litini, Mista Pompeo, ya sanar da wasu sharufda guda 12 ga Iran, wanda a cewarsa idan ta cika su za'a yaye mata jerin takumkumai.

Sharudan guda 12 sun hada da ta janye kwata kwata daga fagen daga a kasar Siriya, sannan ta daina kira ga rusa Isra'ila da kuma daina taimaka wa 'yan Houtsis a Yemen.

Pompeo ya kuma ja kunnen kasashen Turai, da kamfanoninsu dake son ci gaba da hulda da Iran, wadandan ya ce idan suka bijire wa matakin na Amurka, to kuwa su ma za'a dauki mataki akansu.

Tags

Ra'ayi