Mayu 29, 2018 11:20 UTC
  • An Fara Taron Sasanta 'Yan Libiya A Faransa

Yau Talata, an fara wani babban taron muhawara a birnin Paris mai manufar sasanta 'yan Libiya, da zumar samar da hanyoyin shirya zabukan kasar kafin karshen wannan shekara.

Faransa ce dai ta shirya taron a shiga tsakanin Majalisar dinkin duniya, wanda ake fatan zai bude kofar tattaunawa tsakanin 'yan Libiyar don kawo karshen rikici da kasar ke fama da shi.

Ana sa ran taron zai samu halartar dukkan bangarorin dake gaba da juna a Libiyar.

A daya bangare kuma akwai kasashe makobtan Libiya, da kuma wadanda batun ya shafa da aka gayyata a taron wadandan suka hada da Chadi, Nijar, Tunisia, Aljeriya da Masar, sai kujma Congo Brazzaville a daya bangare, dake halartar taron.

Kasar Libiya dai ta kasa samun gindin zama tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar mirigayi Muammar Ghaddafi a cikin 2011.

Tags

Ra'ayi