Jun 23, 2018 11:14 UTC
  • Bin Salman Da Netanyahu Sun Yi Wata Ganawa Ta Sirri A Kasar Jordan

Jaridar Maariv ta haramtacciyar kasar Isra'ila ta ba da labarin cewa yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad bn Salman yayi wata ganawa ta sirri da firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu, a birnin Amman na kasar Jordan.

Jaridar ta bayyana hakan ne a bugunta na jiya Juma'a inda ta ce Bin Salman da Netanyahun sun yi wannan ganawar ta sirri sosai ce a yayin ziyarar da mai ba wa shugaban Amurka shawara na musamman Jared Kushner da kuma manzon musamman na Amurkan a Gabas ta tsakiya Jason Greenblatt suka kai kasar Jordan din.

Duk da cewa dai jaridar ba ta fadi dalilin ganawar ba, amma dai ta ce an yi ganawar ce ba tare da shi kansa sarkin Jordan yana wajen ba duk kuwa da cewa a fadar ce aka gudanar da ganawar.

Wasu majiyoyin dai suna ganin ganawar tana da cikin tsare-tsaren da Amurka da Saudiyya da kuma haramtaciyyar kasar Isra'ila suke gudanarwa da nufin ba da kariya ga 'isra'ila' da tabbatar da tsaronta ta hanyar tilasta wa Palastinawa yin sulhun da ba su so ba.

 

Tags

Ra'ayi