Jul 12, 2018 11:48 UTC
  • Taron Ministocin Cikin Gida Na Kasashen Turai 28

Ministocin harkokin cikin gida na kasashe 28 na kungiyar tarrayar Turai za su soma gudanar da wani taro a birnin Innsbruck da ke a kudancin Austriya

Taron wanda shi ne za a yi a karon farko a karkashin jagorancin Austriya da ta karbi ragarmar kungyar ta EU.

Zai tantance matakan da aka tsayer cikin sabani tsakanin kasashen na mayar da 'yan cirani zuwa Afirka wadanda aka ceto daga tekun Bahrum.

Daga cikin ministocin har'da na Jamus Horst Seehofer wanda ya kalubalanci shugabar gwamnatrin Jamus a game da batun 'yan ci rani a yarjejeniyar da suka cimma a makon jiya.

Ra'ayi