Jul 12, 2018 11:48 UTC
  • MDD: ISIS Ta Yi Sanadiyar Yin Hijirar Mutane 10,000 A  Kudu Maso Yammacin Siriya

MDD ta bayyana cewa kimanin Mutane dubu 10 suka bar gidajensu sanadiyar ci gaba da ayyukan ta'addanci a kudu maso yammacin kasar Siriya, kuma mayakan ISIS din sun hana Mutane da dama ficewa daga yankunan da suke rike da su.

Tashar Telbijin din Aljazera ta nakalto Stephene Dujerik na cewa MDD har ila yau ta samu rahoton kan irin ta'addancin da 'yan ta'adda suke yi a Dar'a da kudu maso yammacin kasar ta Siriya.

Dujarik ya ce rahoton ya ce akwai mutane kimanin dubu goma da suka yi hijra zuwa yankunan Dar'a da Kunaitara saboda ayyukan 'yan ta'adda, kuma wasu da dama na kokarin ficewa daga yankunan, amma 'yan ta'addar na ISIS sun hana su ficewa.

Dujarik ya kara da cewa a halin yanzu akwai 'yan siriya  kimanin dubu 234 da suka yi hijra zuwa yankunan Dar'a da Kunaitara dake bukatar taimakon abinci da kuma magani game da hidimar asibiti.

Tags

Ra'ayi