Jul 12, 2018 17:20 UTC
  • Zanga Zangar Adawa Da Ziyarar Trump A Birtaniya

Rahotanni daga Birtaniya na cewa, an yi zanga zanga a yayin ziyarar da shugaba Donald Trump na Amurka ke yi a kasar.

Bayanai na cewa, ana zanga-zangar ce don nuna adawa da matakin Trump na kin karbar baki.

An  dai jibge jami'an tsaro don sanya ido kan masu zanga-zangar a yayin wannan ziyarar.

A yayin ziyarar dai Trump zai gana da Firaministar Birtaniya, Theresa May wadda ke neman kulla yarjejeniyar kasuwanci bayan ficewar kasarta daga Kungiyar Tarayyar Turai, yayin da shugaban ya ce, kasar Birtaniya na cikin tsaka mai wuya.

Trump zai kuma gana da Sarauniyar Ingila a yayin ziyararsa ta kwanaki biyu.

Tags

Ra'ayi