Jul 20, 2018 10:16 UTC
  • Sin Da Rasha Sun Yi Fatali Da Bukatar Amurka Koriya Ta Arewa

Kasashen Sin da Rasha sun yi fatali da bukatar da Amurka da gabatar shigar gaban MDD, game da dakatar da jigilar man fetur zuwa KOriya ta Arewa.

Kasashen sun bukaci karin lokaci don nazartar bukatar ta Amurka, na sanya takunkumin shigar da Man fetur a Koriya ta Arewa.

Amurka ta bukaci hakan ne saboda a cewarta Koriya ta Arewar ta karya dokar  shigar da man da ya wuce wanda aka kayyade mata shigarwa a kowacce shekara.

Kasashen na Sin da Rasha wadanda ke matsayin kawaye ga Koriya ta Arewa, su ne sahun gaba wajen shigar da man a koriya ta arewa.

Tags

Ra'ayi