Jul 20, 2018 18:11 UTC
  • 'Yan Gudun Hijra Milyan Daya Da Dubu 700 Ne Za A Mayar Da Su Gidajensu A Siriya

Mahukuntar Birnin Moscow Sun Sanar Da Cewa Za su mayar da 'yan gudun hijrar Siriya milyan daya da dubu 700 gidajensu.

Kamfanin dillancin labaran Fars ya nakalto Mikhail Mysynitsov Shugaban Cibiyar Harkokin Tsaro ta Rasha na cewa sun gabatar da shawarwari da dama ga mahukuntan Amurka, kuma a halin da ake cikin suna nazari kansu.

Mikhail ya ce daga cikin wadannan shawarwari akwai batun yadda za a mayar 'yan gudun hijrar Siriya daga kasashen Labnon da Jodan zuwa kasar su, sannan kuma a kafa wata cibiyar hadin gwiwa tsakanin kasashen Rasha-Amurka- Labnon, da kuma Rasha-Amurka-Jodan wadananda za su dauki nauyin mayar da 'yan gudun hijrar na Siriya zuwa kasarsu da kuma yankunansu.

Shugaban Cibiyar Harkokin Tsaro ta Rasha ya kara da cewa Har ila yau Mascow ta gabatar da shawarar kafa kungiyar hadin gwiwa na sake gina kasar ta Siriya, inda tuni magabatan kasashen biyu, wato Rasha da Amurka suka cimma matsaya a ganawar da suka yi a birnin Helsinki.

A ranar Litinin 16 ga watan yulin da muke cikin ne Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin suka gana a birnin Helsinki na kasar Finlande, inda suka tattauna kan batutuwa da dama ciki har da rikicin kasar Siriya.

Tags

Ra'ayi