Jul 21, 2018 12:08 UTC
  • Wani Mutum Ya Farma Matafiya Da Wuka A Cikin Wata Motar Bus A Kasar Jamus

Wani mutum dauke da wuka ya farma matafiya a cikin wata motar bus a yankin arewacin garin Luebeck da ke kasar Jamus, inda ya jikkata matafiya 14 a jiya Juma'a.

Majiyar rundunar 'yan sandan Jamus ta sanar da cewa: Wani mutum dauke da wuka ya farma matafiya a cikin motar bus a garin Luebeck na kasar Jamus a jiya Juma'a, inda ya jikkata mutane 14 amma raunin biyu daga cikinsu ya yi tsanani, don haka an kwantar da su a asibiti domin jinya.

Wasu rahotonni sun bayyana cewa maharin dan shekaru 34 a duniya dan kasar ta Jamus ne da ke zaune a garin na Luebeck, kuma harin da ya kaddamar kan jama'a baya da alaka da tsaurin ra'ayin addini. 'Yan sandan yankin sun yi awungaba da shi domin gudanar da bincike kan lafiyar kwakwalwarsa.   

Tags

Ra'ayi