Jul 24, 2018 12:40 UTC
  • Ana Kara Kai Wa Musulmin Birtaniya Hari

Jaridar Indepandent ta Birtaniya ta buga wani rahoto da yake cewa an sami karuwar kai wa musulmi hari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata

Shugaban kungiyar Tell Mama, Feyyaz Mugahal  ya ce; A cikin shekaru shida na bayan nan kin jinin  da ake yi wa musulmi a Birtaniya yana karuwa. Mughal ya kara da cewa Tun bayan kada kui'ar ficewar Birtaniya daga tarayyar turai a 2016  hare-haren da ake kai wa musulmi ya karu da kaso 475.

Shugagan kungiyar ta Tell Mama ya kuma ce; Maganganun da 'yan siyasa suke yi akan bakanta 'yan ci rani suna taimakawa wajen kara kin jinin musulmi.

Mughal ya zargi kungiyoyin 'yan ta'adda da masu wuce gona da iri na da hannu wajen kai wa musulmi hare-hare.

Tags

Ra'ayi