Aug 14, 2018 19:30 UTC
  • Kasashen Rasha, Turkiya Da Iran Za Su Yi Watsi Da Dalar Amurka A Kasuwancinsu

Kasashen Rasha da Turkiya da kuma Iran za su yi watsi da dalar Amurka a harkokin kasuwancin da suka hada su.

Tashar talajin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya fadi yau a lokacin da suke gabatar da taron manema labarai a birnin Moscow tare da takwaransa na Turkiya jawish Auglo cewa, kasashen rasha da Turkiya gami da Iran za su yi watsi da dalar Amurka a cikin harkokinsu an kasuwanci, sakamakon matakan da Amurka ta dauka na kakaba takunkukumia  kan wadannan kasashe uku.

Amurka a karkashin shugabancin Donald Trup ta ja daga tsakaninta da kasashen Iran da Rasha da kuma Turkiya, inda ta dora musu wasu takunkumai da nufin gurgunta tattalin arzikinsu, lamarin da ya kara kusanto da wadannan kasashe domin daukar matakai na bai daya domin fuskantar Amurka.

Ra'ayi