Aug 16, 2018 12:18 UTC
  • Venezuela Ta Bukaci Kasar Peru Ta Kama Mata Mutanen Biyu Da Take Tuhuma Da Kokarin Kashe Shugaban Kasarta

Ma'aikatar harkokin waje na kasar Venezuela ta bukaci gwamnatin kasar Preu ta taimaka ta kama mata mutane biyu wadanda take zargi da hannu a cikin yunkurin kashe shugaban kasar ta Venezuela wanda bai sami nasara ba.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Venezuela ta bukaci gwamnatin makobciyar kasar Peru da ta taimaka ta kama mata mutane biyu wadanda take tuhuma da hannu cikin yunkurin kashe shugaba Nicolas Madoro a ranar 5 ga watan Augusta da muke ciki. 

Ma'aikatar da kara da cewa ta bawa gwamnatin kasar ta Peru dukkan bayanan da suke da shi dangane da mutanen biyu wadanda ake zaton sun yi amfani da jirgin sama marasa matuki don kashe shugaban Nicolas madoro a lokacinda yake jawabi a wani bukin sojojin kasar a birnin Caracas. 

Gwamnatin kasar Venezuela dai ta zargin kasashen Kolonbia da Amurka da tallafawa wadanda suka yi kokarin kisan

Tags

Ra'ayi