Aug 18, 2018 19:14 UTC
  • Antonio Guterres Ya Yi Kyakkyawan Yabo Kan Marigayi Kofi Anan Tsohon Babban Sakataren MDD

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Marigayi Kofi Anan tsohon babban sakataren Majalisar a kan kansa Majalisar Dinkin Duniya ne.

A sakon ta'aziyyarsa da ya fitar a yau Asabar dangane da rasuwar Kofin Anan tsohon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya: Antonio Guterres babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Irin kwararan matakai da Kofin Anan ya dauka a fagen ci gaban duniya yana fayyace cewa shi kansa yana matsayin Majalisar Dinkin Duniya ne, kuma tarin kyawawan ayyukan da ya gudanar zasu zame masu amfani ga al'umma. 

Gutarres ya kara da cewa: Marigayi Kofi Anan ya kasance mutum mai himma da kwazo a fagen warware matsalolin da suka kunno kai a ko'ina a duniya tare da sanya kafarsa a kowane sako na duniya da nufin gudanar da zaman tattaunawa domin ganin an kai ga samun zaman lafiya da sulhu a duniya.

Bayan fama da rashin lafiya na wani lokaci, a safiyar yau Asabar Allah ya yi wa Kofi Anan rasuwa a asibitin kasar Switzerland yana da shekaru 80 cur a duniya, shi ne babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na bakwai daga shekara ta 1997 zuwa 2006.

 

Ra'ayi