Aug 19, 2018 12:28 UTC
  • Fadan Kasuwanci Tskakanin Amurka A China Ya Fara Tasiri Ga Manoman Amurka

Bayan raguwar shigar da kayayyakin Noma na Amurka zuwa kasar China, farashin kayar noman ya fadi a Amurka.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa gyada na daga cikin kayayyakin noman da kasar Amurka ke shigar da su China, kuma a halin yanzu farashinta ya fadi warwas a cikin kasuwanin Amurka sakamakon fadan kasuwanci da kasashen biyu suka shiga.

Rahoton ya ce cikin watani biyu da suka gabata farashin kayayyakin noman da kasar Amurka ke fitarwa zuwa kasashen ketare ya ragu da kashi 60%, wanda hakan ya sanya a ranar juma'ar da ta gabata kungiyar 'yan kasuwa na bangaren ma'aikatar Noma ta jahar  California suka sanar da cewa hasarar da suke ta yi yayi yawa don haka sun bukaci shugaba Trump da ya kawo karshen wannan yaki na kasuwanci da ya shiga da kasashen Duniya.

A farkon wannan shekara ne Shugaba Trump na Amurka ya shelanta yakin kasuwanci da kasashen Duniya bisa da'awar goyon bayan abinda ake kerawa cikin gida.

Tags

Ra'ayi