Aug 20, 2018 03:26 UTC
  • Al'ummomin Duniya Na Ci Gaba Da Mika Sakonnin Ta'aziyyar Rasuwar Kofi Annan

Gwamnatocin kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa gami da fitattun mutane a duniya suna ci gaba da mika sakonnin ta'aziyyar rasuwar tsohon babban sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan.

Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya nuna kaduwarsa matuka bayan sanar da rasuwar Kofi Annan a jiya, inda ya bayyana rasuwar tasa da cewa na rashi na dukkanin al'ummomin duniya, inda ya bayyana Kofi Annan da cewa shi kansa al'umma ne a cikin mutum daya, domin kuwa ya karar da rayuwarsa ne domin ayyukan al'umma.

A nasa bangaren shugaban kasar Vladimir Putin ya bayyana rashin na Kofi Annan da cewa, babban rashi ne na mutum mai girma, wanda ba za a taba mantawa da ayyukansa ba.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad zarif, ya bayyana rasuwar Kofi Anann da cewa, hakika babban rashi  ne na mutum mai aiki tukuru, wanda ya amfanar da duniya da iliminsa da himmarsa.

Shugabannin kasashen duniya gami da fitattun kungiyoyi na kasa da kasa sunan da kuma fitattun mutane a duniya suna ci gaba mika sakon ta'aziyyar rasuwar Kofi Annan ga iyalansa, da kuma al'ummar Ghana da kuma majalisar dinkin duniya.

Gwamnatin kasar Ghana ta sanar makoki na tsawon mako guda, bayan sanar da rasuwar Kofi Annan a jiya a wani asibiti da ke birnin Bern na kasar Switzerland yana da shekaru 80 a duniya.

Ra'ayi