Aug 20, 2018 03:28 UTC
  • Tsohuwar Daraktan Fadar White House Ta Yi Barazanar Sake Tona Wasu Bayanan Sirri A Kan Trump

Tsohuwar daraktan ayyuka ta fadar White House a kasar Amurka, ta yi barazanar sake tona wasu asirrai dangane da shugaban kasar Amurka Donald Trump, matukar Trump ya nemi ya ci mata fuska.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya habarta cewa,a  zantawar da ya yi da tsohuwar daraktan ayyuka ta fadar White House a kasar Amurka Omarose Manigault-Newman a ranar Asabar, ta bayyana cewa akwai abubuwa da dama na sirri da take da masaniya a kansu da suka shafi Donald Trump wadanda ba ta bayyana su ba, amma idan Trump ya nemi ya takura mata, to za ta fallasa su domin duniya ta sani.

Trump yana zargin Omarose Manigault-Newman da tona wasu daga asiransa, wanda hakan ya sanya shi daukar matakin korarta daga aikinta, kuma tuni wasu daga cikin mukarraban Trump suka fara shirye-shiryen gurfanar da ita a gaban kotu a kan wannan zargi.

Tags

Ra'ayi