Aug 20, 2018 18:12 UTC
  • Antonio Gutterres Ya Yi Kira Kan Goyon Bayan Mutanen Da Ayyukan Ta'addanci Suka Ritsa Da Su

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci nuna goyon bayan ga mutanen da ayyukan ta'addanci suka ritsa da su gami da iyalansu.

A sakonsa da ya fitar dangane da ranar tunawa da mutanen da ayyukan ta'addanci suka ritsa da su a duniya a yau Litinin: Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutterres ya bayyana cewa: Nuna goyon baya ga mutanen da ayyukan ta'addanci suka ritsa da su gami da iyalansu yana daga cikin ayyukan kare hakkin bil-Adama tare da mutunta shi, kuma kyakkyawan aiki ne mai kima.

Gutteres ya kara da cewa: Ci gaba da girmama mutanen da ayyukan ta'addanci suka ritsa da su gami da wadanda suka samu nasarar tsira daga hare-haren ta'addanci lamari ne da zai rusa makirci 'yan ta'adda da suke kokarin raba kan  al'umma tare da cusa kiyayya a tsakaninsu.

Kamar yadda babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya fayyace cewa: Ta'addanci yana daga cikin manyan matsalolin da suka wurga duniya cikin halin kaka-ni ka yi tare da zama babbar barazana ga zaman lafiya da sulhu a duniya.

Ranar 21 ga watan Agustan kowace shekara ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar kasa da kasa domin girmama mutanen da ayyukan ta'addanci suka ritsa da su a duniya. 

Tags

Ra'ayi