Aug 20, 2018 18:13 UTC
  • Paparoma Francis Ya Yi Allah Wadai Da Cin Zarafin Yara Da Malaman Kirista Suka Yi A Kasar Amurka

Shugaban darikar Katolika ta mabiya addinin kirista a duniya ya yi tofin Allah tsine kan cin zarafin kananan yara da wasu malaman addinin kirista suka yi a kasar Amurka.

Kamfanin dillancin  labaran Faransa ya watsa rahoton cewa: A sakon wasika da fadar Vatican ta fitar a yau Litinin yana dauke da tofin Allah tsine da shugaban darikar katolika ta mabiya addinin kirista a duniya Paparoma Francis ya yi kan mummunar aikin assha da wasu daruruwan malaman addinin kirista suka yi da kananan yara a jihar Pennsylvania ta kasar Amurka.

Sakon wasikar ta Paparoma Francis ya kunshi bayanin cewa: Rahoton da ya bayyana a cikin 'yan kwanakin nan cewa a tsawon shekaru kimanin 70 da suka gabata zuwa yanzu an samu daruruwan malaman addinin kirista da laifin yin fyade wa kananan yara tare da lalata musu tarbiyya lamari ne da ke fayyace yadda wasu baragurbin malaman kiristoci suke amfani da matsayinsu wajen rusa kimar addini a idon al'umma, don haka wajibi ne a dauki duk matakan da suka dace wajen hana sake faruwar wannan mummunar dabi'a. Kamar yadda yana kan mabiya darikar ta katolika su yi Allah wadai da irin wannan munanan ayyuka masu zubar da mutunci da kimar dan Adam.

Tags

Ra'ayi