Aug 31, 2018 06:31 UTC
  • Sunan Nabil Rajab A Cikin 'Yan Takarar Lambar Kare Hakkin Dan Adam Ta Turai

An saka sunan shugaban cibiyar kare hakkin bil adama a Baharain Nabil Rajab a cikin ‘yan takarar lambar kare hakkin bil adama ta kasashen turai.

Tashar Lu’ulu’a ta bayar da rahoton cewa, kwamiti na musamman da aka kafa domin fitar da mutane uku da suka taka rawa wajen kare hakkin bil adama a cikin shekara, ya sana sunan Nabil Rajab a cikin jerin sunayen uku da suka cancanci wannan lambar yabo.

Kwamitin ya bayyana cewa, Nabil Rajab ya taka rawar gani maras misiltuwa wajen kare hakkokin bil adama da kuma kare dimukradiyya a Bahrain, wanda sanadiyyar haka tun a cikin shekara ta 2016 ake tsare da shi a gidan kaso.

A kan hakan kwamitin ya ce Nabil Rajab ya cancanci ya zama cikin mutane da za a zaba domin fitar da wanda zai cinye wannan babbar lambar yabo ta kare hakkin dan adam ta nahiyar turai.

Tun a cikin shekara ta 2013 ne aka fara gudanar da wannan shiri na bayar da lambar yabo ta kare hakkin bil adama ta kasashen nahiyar turai, inda a kan zabi mutane da suka taka rawa a wannan fage a duniya domin ba su wannan lambar tare da karramawa.

Tags

Ra'ayi