Sep 05, 2018 09:26 UTC
  • Gwamnatin Spain Ta Warware Wani Cinikin Makamai Da Ta Kulla Tare Da Saudiyya

Gwamnatin kasar Spain ta yanke shawarar yin watsi da wani cinikin makamai da ta kulla da kasar Saudiyya, sakamakon yakin da Saudiyya take kaddamarwa kan al'ummar kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayar da rahoton cewa, gwanatin Spain ta soke cinikin da ta kulla na sayar wa Sudiyya da wasu bama-bamai guda 400 da suke yin amfani da hasken laser.

Gwamnatin Spain ta dauki wannan matakin ne bisa dalilin cewa, bisa zato mafi karfi Saudiyya za ta yi amfani da wadannan makaman ne a kan fararen hula na kasar Yemen, saboda hakan Spain ba za ta zama wani bangare mai taimaka ma Saudiyya wajen kisan fararen hula ba.

An kulla cinikin makaman ne tun a cikin 2015 a kan tsabar kudi yuro miliyan 9, kuma Spain ta sanar da cewa za ta mayarwa Saudiyya da kudadenta bayan rusa cinikin.

Tags

Ra'ayi