Sep 05, 2018 09:27 UTC
  • Bob Woodward: Trump Ya Bayar Da Umarnin A Kashe Bashar Assad Na Syria

Fitaccen dan jarida kuma marubuci a kasar Amurka Bob Woodward ya rubuta a cikin sabon littafin da ya rubuta cewa; a shekarar da ta gabata Donald Trump ya bayar da umanin a yi wa shugaban Syria Bashar Assad kisan gilla.

Jaridar Washington Post da ake bugawa a kasar Amurka ta bayar da rahoton cewa, a cikin littafin nasa mai suna "Fear: Trump in the White House" Bob Woodward ya bayyana cewa, a cikin watan Afrilun shekara ta 2017 da ta gabata, Trump ya kirayi sakataren tsaron Amurka James Mattis da ya shirya yin kisan kisan gilla a kan shugaban Syria Bashar Assad.

Bob ya ce; bayan kammala maganar tasu, Mattis ya ce da mataimakinsa ba za su aiwatar da abin da Trump yake bukata ba.

A jiya fadar White House ta mayar da martani a kan batun, tare da bayyana cewa marubucin ya dogara ne da wasu bayanai na tashar talabijin ta CNBC, wadanda ta harhada ta hanyar wasu tsoffin jami'ai da suka daina aiki tare da Trump.

Ra'ayi