Sep 06, 2018 08:22 UTC
  •  Griffiths:Ba Za A Iya Magance  Rikicin Siriya Da Karfin Soja Ba

Manzon Musaman na MDD kan kasar Yemen ya bukaci gwamnatin da tayi murabus da kungiyar Ansarullah da su zauna ke tebirin shawara domin magance matsalar rikicin kasar.

Tashar talabijin din Aljazera ta nakalto Martyn Griffiths manzon musaman na MDD kan kasar yemen na cewa ba za a iya magance rikicin kasar yemen da karfin soja ba, domin haka, MDD ta dauki duk wani mataki da ya dace na karbar tawagar bangarorin biyu a birnin Ganeva domin tattaunawa.

Griffiths ya ce da farko za su tattauna da ko wani bangare daga cikin su a kebance, sannan suka daga bisani bangarorin biyu damar tattaunawa gaba da gaba.

Manzon musaman na MDD kan kasar Yemen din ya ce manufar tattaunar ta birnin Ganeva shi samar da yarda tsakanin bangororin biyu da aka dakatar da ita shekaru biyu da suka gabata, kuma babu wani sharadi da aka gindayawa bangarorin biyu a wannan zama.

A watan Augustan 2016 ne aka fara tattaunawa tsakanin bangarorin dake rikici da juna na  Yemen a kasar Kuweit, bayan kwashe kwanaki dari ba tare da cimma matsaya, aka dakatar da tattaunawar.

Tags

Ra'ayi