Sep 06, 2018 08:22 UTC
  • Trump Ya Musanta Zargin Bada Umarnin  Kashe Shugaba Asad Na Siriya

Shugaban Amurka Donald Trump ya karyata tattaunawa da ma’aikatar tsaro ta Pentagon ta yi kan bukatar kashe takwaransa na Syria, Bashar al-Assad, bayan wani fitaccen dan jarida, Bob Woodward ya fallasa haka a wani sabon littafinsa da ke nuna irin tabargazar da ake tafkawa a fadar White House. Koda dai Fadar ta White House ta bayyana littafin a matsayin mai cike da karerayi.

A lokacin da yake magana da manema labarai a ofishinsa da ke fadar White House, shugaba Trump ya ce, ko kadan ba su taba tunanin kashe shugaba Assad ba kamar yadda Woodward ya zarge shi a littafin mai suna Fear : Trump in the White House.

Jaridar Washington Post da ake bugawa a kasar Amurka ta bayar da rahoton cewa, a cikin littafin nasa mai suna "Fear: Trump in the White House" Bob Woodward ya bayyana cewa, a cikin watan Afrilun shekara ta 2017 da ta gabata, Trump ya kirayi sakataren tsaron Amurka James Mattis da ya shirya yin kisan kisan gilla a kan shugaban Syria Bashar Assad.

Bob ya ce; bayan kammala maganar tasu, Mattis ya ce da mataimakinsa ba za su aiwatar da abin da Trump yake bukata ba.

Ra'ayi